Home Sashen Hausa An sace ‘Yansanda Goma Sha Biyu 12 a kan hanyar Katsina zuwa...

An sace ‘Yansanda Goma Sha Biyu 12 a kan hanyar Katsina zuwa Zamfara

An sace ‘Yansanda Goma Sha Biyu 12 a kan hanyar Katsina zuwa Zamfara

‘Yan bindiga sun sace ‘yansanda 12 da ke aiki da rundunar ‘yansandan jihar Borno kan hanyar Zamfara-Katsina.

Kampanin dillancin labarai na BBC Hausa ne suka shaida cewa ‘yansansan wadanda dukkaninsu masu mukamin anini ne wato ASPs, na kan hanyar su ne ta zuwa Zamfara domin gudanar da wani aiki a lokacin da lamarin ya faru.

An bayyana cewa daya daga cikin ‘yansandan da ya tsira ne ya ba da rahoton faruwar lamarin, kamar yadda zakuji daga bakin Daya daga cikin Matan ‘yansandan ta bayyana cewa Mijinta ya kira ta tareda bukatar a Jinginar da Gidnsa abiya kudin fansan kafin ya rasa ransa.

Ta bayyana cewa an bukaci da su biya Naira Dubu Dari Takwas akan kowane Daya daga cikin Yansandan a matsayin kudin fansa.

Mai Gudanar da Rahoton yace ya tuntubi Rundunar Yansandan Borno akan Lamarin inda suka ce ya Tuntubi Rundunar Yansandan Jihar Katsina ko Zamfara akan Lamarin su kuma suka bayyana cewa basuda Masaniya akan Lamarin.

Kimanin kwanaki Goma kenan da faruwar Lamarin kamar yadda Matar ta bayyana, amma Labarin bai fito ba sai Yau din nan, Allah ya kubutar dasu cikin Aminci Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...
%d bloggers like this: