AN SACE WATA MATAR AURE DA WANI DIREBA A YANKIN BATSARI.

daga misbahu Ahmad
A ranar lahadin da ta wuce ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun sace wata matar aure mai juna biyu wadda makusantan ta sukace tana gab da haihuwa.
sun sace matar ne a kauyen mai suna Torawa dake cikin yankin karamar hukumar Batsari, Kamar yadda muka samu labarin ‘yan bindigar sun bukaci a basu kudin fansa naira miliyan biyar kafin su sako ta.
A wani labarin kuma an sace wani direban mota mai suna Haro Mali da yaje daukar yalo a wani lambu dake kauyen Torawa, lamarin ya faru ne a cikin daren ranar laraba 17-02-2021 yayin da direban yaje kauyen domin dauko yalo ya kawo kasuwar Batsari wadda ke ci ranar alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here