An sace wasu sojojin ruwa 7 a jihar Edo a Najeriya lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Kaduna daga Delta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun yi nasarar kubutar da biyar daga cikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa a hanyar Sapele zuwa Warri aka sace su, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kwalejin karatun injiniya ta sojin ruwa da ke Sapele.

Jaridar ta ambato wata majiya na cewa sauran sojojin na hannun masu garkuwa da su.

Shi ma mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Kotongs Bello, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi karin haske kan hakan ba.

Najeriya dai na fama da matsalar tsaro da satar mutane domin neman kudin fansa a sassa daban-daban na kasar musamman yankin arewa, inda hatta jami’an tsaro ba su tsira daga sacewar ‘yan bindigar ba.

Ko a baya-bayan nan kungiyar ISWAP ta fitar da wasu hotunan sojojin da ta yi ikirarin ta sace a jihar Yobe da ke arewacin Najeriyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here