Daga Muhammad Inuwa Zaria

A jiya laraba ne 16/03/2022 akaje daura aure daga garin Igabi na jihar Kaduna, zuwa Kano kamar yadda rahotonnu ke tabbatar mana da hakan, “Inda aka nemi sadaki sama ko kasa ba’a Ganshiba.

Sakamakon hakan yasa aka bata lokaci ba’a daura auren ba ana ta kallon kallo a tsakanin juna, Amma daga bisani aka gani a cikin bubban rigan daya daga cikin waliyan amarya, inda yace shi bai ma San yadda akayi kudin suka zo jikinshi ba anan dai aka kori waliyin zuwa waje. Inda aka Kira kanin shi da yazama cikon waliyyan amaryan.

Wannan lamari ya farune a kano a wata unguwa da ake kira da kurna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here