An Sace Kanal Din Soja A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Ansace kanal din soja tsakanin Abuja zuwa Kaduna

An Sace Kanal Din Soja A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani Kanal din sojan Nijeriya bayan sun farmake shi a hanyar Abuja zuwa Kaduna, kamar yadda wadansu majiyoyi daga rundunar sojan Nijeriya suka tabbatarwa da Jaridar Peoples Gazette.

SB Onifade yana kan hanyar tafiya ne da misalin karfe 3:00 na safe a ranar 27 ga watam Satumban shekararnan, inda kuma aka sace shi a wannan rana a daidai kusa gonar Olam (Olam Farms). Har yanzu ba a kama kowa bisa zargin sace shi,

Bayanai sun nuna cewa sojan bai sanya kayan sojinsa ba a yayin da aka sace shi, kamar yadda majiyar soji ta tabbatar.

Majiyarmu ta lura da yadda sace sojan ya sanya firgici a Hedikwatar sojin Nijeriya, wanda har suka gargadi sojoji da su kiyaye tafiye-tafiye a hanyoyin da suke da hadari.

Sace-sace dai a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya zama ruwan dare, inda a koyaushe lamarin ke kara ta’azzara, inda masu garkuwa da jama’a  ke ci gaba da cin karensu ba babbaka a kan hanyar duk da a lokuta da dama jami’an tsaro na sintiri a kan hanyar.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya bai ce uffan ba akan sace jami’in sojan a yayin da aka nemi jin ta bakinsa da yammacin ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here