AN SACE GALADIMAN KUNDURA A KANKIA

@Jaridar taskar labarai

A daren jiya jumma a 19/2/2021 da karfe biyu na dare barayi masu satar mutane suka kai Hari gari kunduru ta karamar hukumar kankia jahar katsina. suka tafi da galadiman garin Alhaji Ibrahim Wanda yake yana Dan shekaru 91 a duniya.kuma baya da cikakkiyar lafiya.

Alhaji Ibrahim mahaifi ne ga babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jahar katsina. Malam kasimu Ibrahim wanda aka fi sani da Simo.

Taskar labarai ta tabbatar da faruwar lamarin ta magana da daya daga cikin ya yansa Wanda ya tabbatar da faruwar abin.
Maharan sun zo bisa babura,kuma a saman suka tafi dashi.har zuwa rubuta rahoton nan maharan basu tuntubi iyalan Galadiman ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here