Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin mambobin kwamatin zartarwa na hukumar Nigerian Upstream Regulatory Commission da ke kula da ayyukan man fetur a ƙasar.

Amincewar ta biyo bayan kammala nazarin wani rahoto da kwamatin majalisar kan man fetur ya gabatar a yau Laraba.

Sabuwar hukumar ta maye gurbin Department of Petroleum Resources (DPR), kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta Pretroleum Industry Act (PIA) ta tanada.

Mambobin da hukumar ta amince da naɗinsu sun haɗa da Isa Modibbo, a matsayin shugaba, da Gbenga Komolafe da Hassan Gambo da Rose Ndong.

Kafin rushe ta, DPR hukuma ce da ke sa ido kan harkokin haƙowa da sayar da man fetur a Najeriya.

Sauran tanadin da dokar PIA ta yi sun haɗa da rushe kamfanin mai na NNPC mallakar gwamnatin Najeriya zuwa na ‘yan kasuwa cikin wata shida tare da sauya masa suna zuwa National Petroleum Corporation.

Kuna iya karanta maƙalar da Umar Mikail ya rubuta kan tanade-tanaden dokar PIA da kuma alfanonsu ga talakan Najeriya a ƙas

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here