An Rusa Shaguna Uku Da Aka Gina Ba Bisa Ka’ida Ba A Katsina.

Hukumar Tsara Birane ta Jihar Katsina URPB,ta rushe ginin wasu shaguna guda uku da akayi ba bisa Ka’ida ba.

Shagunan da aka rushe dai suna kan mahadar unguwar Kofar Yandaka da Filin Polo a nan cikin birnin Katsina kuma Babban jami’in Tsara Birane a Hukumar TPL.Umar Ali ne ya jagoranci aikin.

Kamar yadda TPL.Umar Ali yace,tuni hukumar ta bayar da takardar umarnin janyewa daga wurin ga Wanda ya gina shagunan bai aikata hakan ba,har ta kai ga an bashi takardar sanar da shi matakin rushe Shagunan wanda har a lokacin bai tashi daga wurin ba.

Yace Hukumar ta tsara rusa Shagunan a ranar 23 ga watanda ya gabata sai dai an sake bashi tazara har zuwa ranarda aka rusa Shagunan amma ya bijirewa umarnin hukumar.

TPL.Umar Ali yace gina Shagunan a wannan wuri yana haifar da hadurra a kowace rana,hakan ya sanya al’uma suka kai korafi ga hukumar don ta kawo dauki.

Shima a nashi bangaren,Jami’i a Hukumar TPL.Najib Zakka yace wannan shine karo na biyu da aka rusa shagunan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here