Home Sashen Hausa An rufe guraren tsugunar da ƴan gudun hijira a Katsina

An rufe guraren tsugunar da ƴan gudun hijira a Katsina

An rufe guraren tsugunar da ƴan gudun hijira a Katsina

Governor Aminu Bello Masari Katsina state

An rufe guraren tsugunar da ƴan gudun hijira a Katsina

AMINU BELLO MASARI

Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya ta sanar da rufe dukkan sansanonin da ta buɗe don tsugunnar da mutanen da rikici ya raba da gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji.

Hukumomi sun ce sun mayar da dubban mutanen zuwa garuruwansu ne, bisa hujjar ingantuwar harkokin tsaro a sassan Katsina.

Sansanonin na ɗauke da sama da mutane dubu 27 a ƙananan hukumomin Andume da Faskari da ƙankara da kuma Jibiya.

Shugaban kwamitin kula da ƴan gudun hijira na jihar ta Katsina Sani Aluyi Ɗanlami ya shaidawa BBC gwamnatin na daukar matakan yaki da ta’addanci da kan haifar da barazana a jihar.

Jihar dai na ciki jihohin arewa maso yamma na Nijeriya da ke fama da hare-haren ‘yan fashin daji da satar mutane don kuɗin fansa.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: