Gwamnan Jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari ya jagoranci rantsar da sabbin Shugabannin kananan hukumomi da aka zaba a ranar Litinin.

An dai yi taron rantsarwar ne a babban wurin taro dake gaban gidan gwamnatin jihar a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu.

Babban jojin jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya rantsar da sabbin Shugabannin kananan hukumomin.

Da yake jawabi ga sabbin Shugabannin, Gwamna Masari ya ja hankalin su da su maida hankali wajen inganta hanyoyin tattara kudaden shiga da Kuma kashe su.

Gwamnan tun da farko ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina bisa yadda yace ta gudanar da zabukan kananan hukumomin da mazabu na jihar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Bayan rantsar da sabbin Shugabannin a hedikwatar jihar, Katsina Post ta samu cewa shugabannin sun dunguma zuwa kananan hukumomin su inda suka rantsar da mataimakan su da kansilolin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here