Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su dage wajen karowa da zurfafa Ilmin su domin karin nagartar aikin da suke gudanarwa da kuma samun cigaba wajen aikin cikin sauki kuma kan kari.

Gwamnan yayi wannan kiran ne yau yayin da ya rantsar da sabbin Manyan Sakatarori guda shidda a babban dakin taro na fadar gwamnati dake nan Katsina.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa, duba da yadda tsarin rayuwa ke canzawa ta fuskar da komai sai an shigar da ilmi mai zurfi, ya zama wajibi ma’aikatan su zage damtsin wajen samo Ilmin da za su tafi tare da zamani ko kuma zamani ya tafi ya bar su.

Da ya juyo ta wajen wadanda aka rantsar din, Gwamna Masari yayi kira gare da su rike amanar aikin domin ta haka ne kawai za suci ribar aikin har zuwa bayan sun ajiye shi.

Wadanda aka rantsar din su ne;

Halliru Liman Duwan
Hukumar kula da Ilimi mai Zurfi

Abubakar Muhammad Gege
Ma’aikatar Kula da Muhalli

Sani Bala Kabomo
Ma’aikatar Yada Labarai

Injiniya Abdu Usman
Ma’aikatar Kula da Albarkatu

Mustapha Abdu Saulawa
Sashen Kula da Hidimar Baki

Dokta Aminu Waziri Garba
Ma’aikatar Ayyukan Gona

Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu, Babban Jojin Jiha Maishari’a Musa Danladi Abubakar, Alkalin Alkali Dokta Muhammad Kabir Abubakar, Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Muntari Lawal Katsina, tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da sauran manyan jami’an Gwamnatin Jiha suka halarci wannan bukin rantsuwa.

Muna rokon Allah Yayi masu jagoranci, kuma Shi mana maganin abinda ya ishe mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here