An nada tsohon Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniya a Najeriya
An naɗa tsohon sarkin Kano Sanusi na II a matsayin jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.
Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoraci naɗa tsohon sarkin a matsayin Khalifa a babban taron ɗariƙar da aka gudanar a jihar Sakkwato.
Sarki Sanusi na II yanzu ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya
Tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu ba a naɗa sabon Khalifa ba a Najeriya.
Taron ya samu halartar manyan shugabannin ɗarikar Tijjaniya na Najeriya da wajen ƙasar da suka haɗa babban malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
