An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU)

Mukamin na ‘Chancellor’ na jami’ar ta CUU ta kasar Uganda, na daya daga cikin muhimman karramawa ta kasa-da-kasa da tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan ya samu, tu bayan saukarsa daga mulkin Najeriya a shekarar 2015.

Jami’ar ta Cavendish wadda ba ta gwamnati ba ce, tana daya daga cikin manyan jami’o’i a nahiyar Afirka.

An bude jami’ar ne a shekarar 2008, inda ta soma gudanar da ayukan ta a karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Zambia, marigayi Kenneth Kaunda, wanda ke matsayin ‘Chancellor’ na jami’ar.

Jami’ar ta CUU tana da hadin gwiwa da kwalejin Cavendish da ke birnin London, da jami’o’in Cavendish da ke kasashen Tanzania da Zambia, haka kuma ta soma yaye dalibai ne a shekarar 2011.

A shafinta na sadarwa na Facebook, jami’ar ta bayyana farin ciki da marhabin da samun sabon shugaban, inda kuma ta yi masa fatan samun nasara a sabon aikin na shi.

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan dai na ci da samun karbuwa da farin jini a matakin kasa-da-kasa, kama daga nahiyar Afirka har ya zuwa matakin duniya.

Masu fashin baki na ta’allakawa lamarin ne da dattaku da jaruntakar da ya nuna, na mika mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari, bayan da aka ba da sanarwar ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

Jonathan ya yi aiki a zaman manzon wanzar da zama lafiya na kungiyoyin Afirka da ma na Majalisar Dinkin Duniya a lokuta da dama a kuma kasashe daban-daban.

Na baya-bayan nan shi ne aikin shiga tsakani a rikicin jama’ar kasar Mali da gwamnatin mulkin soji da ta hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hula a wani juyin mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here