Advert
Home Sashen Hausa An naɗa Sheikh Ibrahim Bin Sheikh Ɗahir Usman Bauchi a matsayin Khalifan...

An naɗa Sheikh Ibrahim Bin Sheikh Ɗahir Usman Bauchi a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

An naɗa Sheikh Ibrahim Bin Sheikh Ɗahir Usman Bauchi a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

Aliyu Samba.

Sanarwar ta fita ne a wata takarda da sahannun Khalifan Daidai Tijjaniyya Sheikh Muhammad Mahi Sheikh Ibrahim Inyass. A cikin takardar an ayyana Sheikh Ibrahim Bin Sheikh Ɗahir Usman Bauchi a matsayin Khalifan Tijjaniyya a Najeriya tare da Sheikh Tijjani Auwal Kano a matsayin naqib (Mataimakin) sa.

A watan da ya gabata ne aka samu yaɗuwar wani labari da ke nuna cewa an naɗa tuɓaɓɓen Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifa yayin bikin maulidin Shehu Ibrahim da akai a garin Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya, saidai daga baya Khalifan Shehu Inyass ya bayyana cewa ba a yi wannan naɗi ba.

A cikin wani faifan bidiyo mai motsi an ji khalifan yana cewa al’amarin naɗa Khalifa a ƙasa irin Najeriya al’amari ne babba da yake da buƙatar a zauna a kuma tantance da masu hannu da tsaki.

Sheikh Ibrahim Ɗahir Usman Bauchi shine tabbataccen khalifan Tijjaniyya a Najeriya bayan Marigayi Khalifa Isyaka Rabiu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU)

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU) Mukamin na ‘Chancellor’ na jami’ar ta CUU ta...

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan”

LABARI DA DUMI-DUMIN SA! "Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan" Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya labule da...

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya A ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021,...

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot I am sharing this with Friends because the Western MainStream Media (MSM) will NEVER show you...
%d bloggers like this: