An naɗa janar din soji 15 da za su mulki Chadi

An sanar da wadanda za su jagoranci gwamnatin riƙo a kasar Chadi ta tsawon watanni 18, bayan mutuwar katsahan da Shugaba Idris Deby Itno ya yi a ranar Talata.

Tuni sojojin suka sanar cewa dan marigayin janar Mahamat Idris Deby Itno, wanda ake kira da Mahamat Kaka mai shekara 37- shi ne zai jagoranci kasar.

Janar Mahamet ya fitar da wata sanarwar, tare da jera sunayen masu muƙamin janar din soji 14 da za su hadu don jan ragamar kasar

Wata ma’aikaciyar sashen BBC Monitoring ta wallafa kwafin sanarwar a shafinta na Twitter.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here