Akasin labari mai daɗi da jama’a suke dakon ji, ta sauya zane a halin yanzu dai an damka Bakin Balarabe hannun Jami’an Ƴansanda a jihar Nasarawa.

Idan dai ba’a manta ba Bakin Balarabe ya damka Raƙumin shi ga Sabon Shugaban Jam’iyya APC Abdullahi Adamu da niyyar tayashi murna, sai dai maimakon samun tukuici mai gwaɓi Bakin Balarabe ya samu tukuicin Naira Dubu Ɗari ne kaɗai, lamarin da baiyima Bakin Balarabe daɗi.

Wannan lamarin dai yasa ya sauya tunanin shi tare da cewa ya fasa bada wannan Raƙumin nashi ga Shugaban Jam’iyyar tasu.

Bakin Balarabe dai yayi tattaki ne da Raƙumin shi tun daga Katsina har zuwa Abuja wajen babban taron Jam’iyya domin Karrama ita Jam’iyyar tashi ta APC yayin convention.

Da muke zantawa dashi yace kuɗin da aka bashi ko kuɗin abincin Raƙumin basu kaiba balle kuma kuɗin Raƙumin kanshi da sauran Dawainiyar da yayi tun daga Katsina har zuwa Abuja kafin kuma daga nan ya yanki hanya zuwa Nasarawa.

Ibrahim yace Shugaban Jam’iyyar ya bashi Dubu Ɗari da Umarnin cewa a ɗauki Raƙumin akai shi Gidan Gona yayin da shi kuma ya kama hanyar zuwa Abuja, sai dai Ibrahim yace hakan bata saɓuba dan haka yayi Yunƙurin tafiya da Raƙumin shi yayinda su kuma yaran Shugaban Jam’iyyar suka lallai hakan kuma ba zata yiyu ba.

Ya zuwa yanzu dai Lambar wayar Bakin Balarabe idan an kira tana ta kaɗawa amma ba’a ɗauka 08141918731.

Muna mashi fatan samun mahita akan wannan Lamarin Amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here