Advert
Home Sashen Hausa An Maye Gurbin Muƙamin Abba Kyari Da Tunji Disu

An Maye Gurbin Muƙamin Abba Kyari Da Tunji Disu

YANZU-YANZU: An Maye Gurbin Muƙamin Abba Kyari Da Tunji Disu

Babban Sufeton Janar na ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya amince da naɗin DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT)

Wannan na nufin shi zai maye gurbin Abba Kyari da aka dakatar kan zargin rashawa.

Sanarwar da ke ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran rundunar, CP Frank Mba ta ce DCP Disu zai kama aiki gadan-gadan ba tare da ɓata lokaci ba.

Kuma a cewar sanarwar IGP Alkali na saran sabon shugaban ya nuna ƙwarewa da jagoranci wajen aiwatar da aikinsa da sauke nauyin da aka ɗora masa.

Kafin naɗin DCP Disu wannan mukamin, shi ne tsohon kwamandan kai agajin gaggawa na Rapid Response Squad (RRS) ta jihar Legas. Kuma ya rike mukamin mataimakin kwamshina a sashin ayyuka na rundunar a hedikwatarta ta Abuja.

Sannan ya rike mukamai daban-daban da ayyuka a fanoni da dama na rundunar.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...

REHABILITATION WORK DONE AT THE EKEHUAN ARMY BARRACKS IN BENIN, EDO STATE!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/259649386251586/