AN KUBUTAR DA MUTANE (77) DAGA HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE.

Da yammacin yau Alhamis 07/01/2021 Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya amshi mutum (77) da aka kubutar dasu daga hannun masu garkuwa da mutane. Adadin mutanen da aka kubutar dasu daga hannun masu garkuwa da mutane ya kama mutum (104) bayan kubutar da Daliban Makarantar Kimiyya ta Gwamnati dake Garin Kankara.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya amshi mutanen, Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana “cewa hanyar da akabi aka kubutar da Daliban Makarantar Kimiyya ta Gwamnati dake Garin Kankara itace akabi aka kubutar da wadannan mutane daga hannun masu garkuwa da mutane, ba tare da an biya kudin fansa ko sisin kobo ba.inji shi

Gwamnan ya cigaba da “cewa mutanen an dauke su daga wurare daban, daban, wasu an dauke su daga yankin Batsari, wasu daga yankin Jibia, wasu daga yankin Faskari, wasu daga yankin Dandume, wasu daga yankin Sabuwa, wasu daga yankin Batagarawa, wasu ma daga makwabciyar Jihar mu, Jihar Kaduna”.

Wannan yana cikin kokarin da muke don kawo karshen wannan matsala da muke fama da ita. Daga karshe Gwamnan ya ba mutanen da aka kubutar hakuri tare da basu tabbaci da yaddar Allah Gwamnati na iya bakin kokarin ta don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Katsina kamar da, Gwamnan “ya yi addu’a, idan mutanen dake aikata wannan mummunar dabi’a masu shiryuwa ne, Allah ya shiryar dasu, idan kuma ba masu shiryuwa bane, Allah kai kasan yadda zakayi dasu Allah kayi mana maganin su.

Kwamishinan Rundunar yan Sanda ta Jihar Katsina CP. Sanusi Buba da Biriged kwamanda na Jihar Katsina suka mika mutanen ga Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari bayan an dauko su daga inda masu garkuwa da mutanen suka aje su bayan sun sako su daga inda suke tsare dasu.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
07, January 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here