Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram guda 75 tare da ƙwato manyan bindigogi cikin kwana uku.
Sai dai soja uku sun rasa rayukansu sannan wasu huɗu sun jikkata, a cewar sanarwar da muƙaddashin daraktan sashen bayanai na rundunar Birgediya Janar Benard Onyeko ya fitar a yau Talata.
Yayin fafatawar da aka yi tsakanin Laraba, 28 zuwa Asabar 31 ga Oktoba, dakarun rundunar Lafiya Dole sun yi nasarar ƙwace motoci masu bindigogin da ke sarrafa kansu guda huɗu da makaman harbo jirgin sama uku da kuma sauran manyan makamai.

Kazalika, sanarwar ta yaba wa dakarun rundunar “bisa jajircewarsu da ƙwarewar aiki tun daga lokacin da aka ƙaddamar da ita”.
A ranar Lahadi mayaƙan Boko Haram sun kashe mutum aƙalla bakwai a harin da suka kai ƙauyen Takulashe da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
An kafa rundunar Lafiya Dole ne domin kakkaɓe ‘yan ƙungiyar Boko Haram da ƙawayenta a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Rikicin wanda aka shafe shekara sama da 10 ana yi, ya haddasa mutuwar fiye da mutum 36,000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya sannan ya raba miliyoyi da mahallansu.