An kashe ‘yan bindiga da dama a Jihar Imo.

Wata tawagar jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun kashe ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ne da dama a Jihar Imo da ke kudancin Najeriya ranar Alhamis.

Rahotanni na cewa an kashe aƙalla ‘yan bindiga takwas yayin da suka yi yunƙurin kai hari a ofishin ‘yan sanda na Orlu.

Jami’an tsaron sun kuma ƙwace motoci kusan bakwai na ‘yan bindigar da suka yi amfani da su yayin harin, waɗanda ake zargin na sata ne.

Wata mota
Daniel EkeomaCopyright: Daniel Ekeoma
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda suka ɗaura ɗamarar yaƙin.

Mazauna yankin sun ce an shafe awanni ana fafatawa tsakanin ɓangarorin biyu, abin da ya sa suka kasa barci da idonsu rufe.

Fafatawar na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Abutu Yaro ya fara aiki a jihar.

A watan da ya gabata ne wata tawagar jami’an tsaron ta kashe wani kwamandan ƙungiyar ta IPOB mai suna Ikonso da wasu mayaƙansa guda shida.

‘Yan ƙungiyar ta IPOB wadda ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya sun sha kai hare-hare kan ‘yan sanda tare da kuɓutar da waɗanda ake tsare da su a jihohin yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here