Advert
Home Sashen Hausa An kashe sojojin Najeriya 10 a Jihar Borno

An kashe sojojin Najeriya 10 a Jihar Borno

An kashe sojojin Najeriya 10 a Jihar Borno

Sojojin Najeriya

Aƙalla sojojin Najeriya 10 ne suka mutu yayin wani artabu da mayaƙan ƙungiyar da ke da alaƙa da IS a Alagarno da ke Jihar Borno, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai hare-hare guda uku a kan dakarun na Najeriya cikin wata sanarwa a jiya Talata, inda ta ce ta kashe sojoji bakwai ranar Litinin tare da kama wani guda ɗaya.

Wasu majiyoyin tsaro sun faɗa wa AFP cewa sojoji 10 ne suka mutu bayan dakarun Najeriyar sun kai wa sansanin ƙungiyar ISWAP hari ranar Litinin a Alagarno.

“Mun rasa soja 10 a faɗan kuma ‘yan ta’adda sun ɗauke ɗaya,” in ji majiyar. An kama sojan ne yayin da yake neman tsira sakamakon ruwan wutar da ‘yan bindigar suka yi musu, a cewarsa.

“An fafata sosai kuma an kashe ‘yan bindigar su ma, amma duk da haka sun rinjayi sojojin,” a cewar majiya ta biyu.

Mayaƙan ƙungiyar sun ƙwace mota huɗu da suka haɗa da motar silke da kuma na zirga-zirga.

Ƙungiyar ta wallafa wasu hotuna tana iƙirarin cewa sojan da ta kama ne da gawarwakin waɗanda ta kashe da kuma motocin da ta ƙwata daga hannunsu.

A cewar ƙungiyar, cikin ɗaya daga hare-haren da ta kai, ta yi wa sojoji kwanton-ɓauna a kan titin Gamboru zuwa Dikwa, inda ta kashe soja huɗu.

Garin Alagarno mai nisan kilomita 150 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ya kasance matattarar ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram a 2016 kuma take cin gashin kanta.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 36,000 a yankin arewa maso gashin Najeriya, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Ɗan Namadi Sambo ya nemi a dawo masa da kuɗaɗensa bayan shan kaye a zaɓen fidda-gwani

Adam Namadi, dan tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo, ya nemi wakilan zaɓe wato su dawo masa da kuɗin da ya ba su bayan...

ZAƁEN FITAR DA GWANI A KATSINA: Duk wanda yaci Firamare Election Zamu mara masa baya… -Yantakara-

Masu nemqn tsayawa takarar Gwamnan jihar Katsina sunyi wani Zama mai kama da na Sulhu a gidan Gwamnatin Katsina tare da Gwamna Aminu Bello...

BANKIN NIRSAL YA SAMA QA MANOMAN KAYYAMA GINDIN ZAMA A KWARA #GaskiyarLamarinNijeriya

Ko kun san Gwamnatin Shugaba Buhari ta hannun Bankin Bunƙasa Manoma (NIRSAL) ta tallafa wa ƙungiyar manoma ta Kaiama Integrated Agro Geo-Cooporative ta hanyoyi...

“Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku, Kuji tsoron Allah”…..Saƙon Ɗan takarar Gwamna, Sanata Sadiq Yar’Adua ga Delegate.

"Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku, Kuji tsoron Allah".....Saƙon Ɗan takarar Gwamna, Sanata Sadiq Yar'Adua ga Delegate.   Zaharaddeen Ishaq...

Wata Sabuwa: Maryam Abacha Ta Maka Gwamna El-rufa’i A Kotu

Rahotannin da ya ke riskenmu yanzu sun bayyana cewa matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Sani Abacha, wato Maryam Abacha ta maka Gwamnatin Jihar Kaduna...
%d bloggers like this: