Advert
Home Sashen Hausa An Kashe Sama Da Mutum 22 Kuma Ana Binsu Bashin Miliyan 70

An Kashe Sama Da Mutum 22 Kuma Ana Binsu Bashin Miliyan 70

Comrade Yahaya M Abdullahi

Yan bindiga kashe mutum 20 da tsakar rana a ƙauyen Inonon Madawaki, dake ƙarƙashin ƙaramar Hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sun kashe mutane 18 a lokaci guda, sannan suka jikkata adadi mai yawan gaske wanda daga baya wasu daga cikin su suka mutu bayan mummunan harbin da aka musu a jiki.

Wani wanda ya samu kubuta daga harin ya zartar da mu cewa: a garin Sabuwa mutum 2 suka kashe, suka kuma jikkata Wasu da dama.

Ya kara da cewa “Sojoji guda 5 ne gaba daya ƙaramar Hukumar Sabuwa kuma kowa dake cikin garin Sabuwa yasan da hakan, sai kuma Ƴan Banga waɗanda ke tsayawa idan Ɓarayin sun shigo”

”Shigowar da suka yi ƙarfe biyar na yammacin ranar talata, suka shigo kamar yanda suka yi alƙawari in ba’a kai musu Kuɗin da suka bukata ba, kuma da suka tashi zuwa basu zo ta ɓangaren da suka saba zuwa ba sai suka zo ta bangaren Hayin Gwari suka shigo” inji shi.

“Akwai Ƙauyukan dake nan wajen kafin shigowa garin amma sun tashi dukkan ƙauyukan dake nan hanyar, danko ce kadai ba’a Tada ba, daga waɗanda aka kashe sai waɗanda suka tashi da kansu ganin kashe-kashen yayi yawa. Da suka shigo garin Sabuwa kuwa, Wallahi Mutane da dama sunyi asara, domin gudu kawai aka dinga yi har nima nayi gudu sosai domin tsira da rayuwana kuma ana tsakiya da cin kasuwa suka shigo.” Inji shi.

Ya kara da cewa “Akwai Ma’aruf mun san shi sosai kamar ma yana da Ɗan matsala a kansa, sun kashe shi da suka shigo, saboda kowa na gudu shi kuma lokacin yake ƙoƙarin shigowa ma cikin garin a nan suka tarar dashi, sai bayan da suka tafi aka gano shi aka masa sallah.”

Bayan yan bindigar sun saki wani da suke tsare dashi, sai suka jaddada masa akan lallai yazo ya faɗa wa mutanen garin cewa ana Binsu Bashin wannan Kuɗin har yanzu wanda hakan ne ma yasa suka zo a ranar Talata domin bin bashin Miliyan saba’in ɗin.

Ya cigaba da cewa “Rufe Network Ɗin garin Sabuwa ba abunda ya ƙara mana sai tashin hankali da kashe-kashe da kullum ake mana kamar kiyashi haka ake kashe mutane a yankin Sabuwa, in akwai Network garin dake gaba zasu kira mu amma yanzu babu, komai a garin ya jagwalgwale mana kawai dai muna rayuwa ne.”

©Jarida Radio
4/11/2021

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yansanda A Katsina Sun Chika Hannu Da Yan Kungiyar Asiri Biyu

Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina ta kame wasu matasa biyu da make zargin yan Kungiyar Asiri ne. Kamar yadda Jami'in Hulda da Jama'a na...

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...