An kashe mutum biyu a wurin zanga-zangar #ENDSARS a Edo

An kashe mutum biyu, an raunata wasu da dama yayin wata arangama tsakanin masu zanga-zangar #ENDSARS da kuma ‘yan daba a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa ‘yan dabar sun far wa masu zanga-zangar ne da adduna da wasu munanan makamai yayin da suke gangami a Dandalin King da ke jihar.
Domin ramuwar gayya, matasan da ke zanga-zangar sai suka afka gidan tarihin birnin Benin inda suka samu masu zanga-zangar, sai faɗa ya ɓarke, kamar yadda jaridar ta ruwaito.
Ko a ranar Laraba sai da aka samu shigen irin wannan lamarin a Abuja babban birnin Najeriya inda ‘yan daba suka afka wa masu zanga-zanga har suka lalata musu motoci.
Haka zalika ‘yan daban sun kai hari ga wasu masu zanga-zangar a Legas inda suka tarwatsa su.