Gwamnatin jihar Kaduna arewacin Najeriya ta sanar da cewa an kashe kasurgumin wanda ake zargi da jagorantar satar mutane a kan hanyar Kaduna-Abuja Nasiru Kachalla

Kwamishinan Tsaro na jihar Samuel Aruwan ya ce an kashe Kachalla sakamakon wata hatsaniya da ta kaure kan yadda za su raba shanun sata a tsakanin mutanen Kachallan da wani gungun masu aikata laifi a dajin da ke iyakar Kajuru da Chikun na jihar Kaduna. Shin ya ku ka ji da yadda aka samu rahotan ‘yan ta’adda sun fara kashe junansu?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here