An Karkare Taron Karawa Juna Sani Na Media Forum Katsina.

Daga A.I Musa.

A ranar Juma’ar nan 26 ga Sha’aban, 1412H (9 ga Afrelu 2021), Media Forum Katsina ta kammala wani taron karawa juna sani, taron da ta shafe Yini biyu tana gudanarwa a Katsina.

Taron mai taken ‘Career In Technology’ a turance, wanda Fasihin Masanin na’ura mai kwakwalwa daga kasar Ghana, Mr Ishaq Abubakar ya gabatar, ya haifar da da mai Ido ya kuma fa’idantar.

A Yinin Farko na taron, Matashin Masanin Kwanfutar, ya gabatar da Jawabi ne a kan “Hanyoyin Da Mutum Zai Samu Kudi A Zaurukan Sada Zumunta Na Zamani (Social Media)” inda ya yi bayani mai tsawo kuma mai gamsarwa inda ya warware zare da bawa a kan yadda mutum zai ribaci harkar.

A Yini na biyu a taron (ranar karkarewa), ya yi Jawabi ne mai Taken “Yadda Za Ka Gabatar Da Abin Da Ka Kware A Kansa A Intanet” inda nan ma ya koyar tare da kwatanta yadda ake gina ‘Shafin Yanar Gizo’ tayadda za ka iya Tallata abin da ka kware a kansa ga duniya baki daya kuma ya kar6u ya yi Kasuwa har ka samu zunzurutun Kudade a kansa.

A yayin gabatar da taron na Kwanaki biyun dai, Membobi Media Forum din ne suka halarta, sun kuma mai da hankali bakin gwargwado wanda har hakan ya sa Matashin Masanin ya yaba kokari da kuma kwazonsu.

Daga Karshe, Mr Ishaq, ya yi wa Membobin dandalin na Media wani albishir da cewa, duk wanda ya hu66asa ya ci gaba da mai da hankali ta hanyar yawaita jaraba abubuwan da ya koyar a aikace ba tare yin rauni ko sa wasa a ciki ba, to zai ba shi wata dama ta yin karatu da samun shaidar karatu(Certificate) a wata Jami’a ta wannan tsarin a kyauta, shaidar da in ba ta hanyarsa ba sai an kashe makudan kudade kafin a same ta.

Daga bisani, jim kadan da kammala taro ne, aka yi addu’a tare da Hotunan tarihi aka sallami jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here