Advert
Home Sashen Hausa AN KAMA WATA MATA MAI SAFARAR MAKAMAI DA MAKUDDAN KUDI A BATSARI.

AN KAMA WATA MATA MAI SAFARAR MAKAMAI DA MAKUDDAN KUDI A BATSARI.

A ranar litanin 19-07-2021 da misalin 09:00am aka kama wata bafulatana mai suna Aisha Nura, wacce ‘yar kauyen Baranda (Rugar Fulani) ce dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, matar mai kimanin shekaru 27 an kama ta da tsabar kudi har naira miliyan biyu da dubu dari hudu da biyar, (N2,405,000). Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bakin mai magana da yawunta SP Isah Gambo ya bayyana cewa sunyi nasarar kama matar ne sakamakon bayanan sirri da suka samu, inda suka cafke ta a cikin garin Batsari ta jihar Katsina, lokacin da take neman dan acaba da zai kai ta kauyen Nahuta. Da aka bincike ta ne aka same ta da wadannan kudi wanda ake tsammanin tana safarar makamai ne ga ‘yan bindiga na yankin jihar Kaduna.

Daga karshe ta bayyana ma rundunar ‘yan sanda cewa, ita matar wani dan bindiga ce mai suna Nura Alhaji Murnai wanda yake karkashin dabar Abu Radda, kuma shine(Radda) ya tura ta dajin Kaduna domin ta karbo masa kudin wuri abukkan huddar su dake can.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: