An kama wani matafiyi dauke da kokon kan mutum da hannuwa a Kwara

DLC

Rundunar ‘yansanda a jihar Kwara ta ce ta cafke wani mutum dauke da kokon kai da ma hannuwan mutum boye cikin jaka a wata motar bas ta haya da ta tashi daga Ajase-Ipo zuwa Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda a jihar, SP Okasanmi Ajayi, wanda ake zargin, Kehinde Moses, ya amsa cewa ya kashe mai laifin, Mohammed, don yin tsafi a Ajase-Ipo, karamar hukumar Irepodun ta jihar.

Ya ce an cafke wanda ake zargin ne a ranar Litinin bayan da ‘yansanda suka tsayar da motar domin bincike a kan hanya, ya kara da cewa abokin aikata laifin na Moses ya tsere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here