– Wanda ake zargin yana tare da wasu ‘yan mata shida ‘yan shekara 16 zuwa 20 kuma duk a shirye suke su tafi kasar Burkina Faso, an kama su ne a yankin Gboko na jihar Benue a ranar 5 ga watan Janairun 2022.

Jami’an tsaron na Civil Defence da sauran jami’an tsaro na Najeriya reshen jihar Benue, sun kama wani da ake zargi da safarar mutane mai suna Mnena Kwaghmande.

Wanda ake zargin yana tare da ‘yan mata 6 ‘yan shekara 16 zuwa 20 kuma duk a shirye suke su tafi Burkina Faso, an kama su ne a yankin Gboko na jihar Benue a ranar 5 ga Janairu, 2022.

Kwamandan NSCDC a Benue, Philip Okoh, ya bayyana wanda ake zargin da wadanda abin ya shafa, inda ya ce an dauko ‘yan matan ne daga karamar hukumar Vandeikya ta jihar.

Okoh ya bayyana cewa wanda ake zargin da aka yi masa tambayoyi ya yi ikirarin cewa ya shaida wa iyayen ‘yan matan cewa za su taimakawa wata mata a gidan abincinta da ke Burkina Faso.

“A baya mun kama gogaggen mai fatauci Inda yake yaudarar iyayen ta hanyar gamsar da su cewa za su fitar dasu waje kasuwanci.

“Bincike ya nuna cewa suna kai su Burkina Faso.

Okoh ya gargadi iyaye da su guji sakin ‘ya’yansu ga mutanen da suka yi alkawarin kaisu kasashen ketare, inda ta ce hakan kan barna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here