‘An kama Sunday Igboho a Cotonou yana ƙoƙarin guduwa Jamus’

Sunday Igboho

Rahotanni daga Najeriya na cewa an kama mai fafutukar kafa kasar Yarbawa zalla a shiyyar kudu maso yammacin kasar wato Sunday Adeyemi wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Labarin kamen nasa na zuwa ne makonni uku bayan da jami’an ƴan sandan ciki na ƙasa suna yi dirar mikiya a gidansa da ke Ibadan.

Sun yi hakan ne kwana uku gabanin ranar gudanar da wani gagarumin gangamin ‘yan kabilar Yarbawa da ya kira a birnin Legas.

To bayanan da Haruna Tangaza na BBC Hausa ya tattara daga majiyoyin daban-daban na nuna cewa an kama Sunday Igboho ne jiya da yamma a filin jirgin sama na Cotonou na kasar Benin mai makwabtaka da Najeriya.

Manyan kafafen watsa labarai daban-daban a Najeriya sun ce an kama shi ne yana ƙoƙarin hawa jirgi domin arcewa zuwa kasar Jamus, bayan da su jami’an ƴan sandan ciki suka ayyana shi a zaman wanda ake nema.

To ko muna da labarin a inda yake yanzu?

To bisa rahotannin da BBC ta samu dai yau ne aka ce su hukumomin kasar ta Benin za su hannunta shi ga mahukuntan Najeriya.

Sai dai abin babu tabbas akai shi ne ko kawo zancen nan da muke an riga an miƙa shi ko kuma a’a.

Sai dai jaridu daban-daban sun ambato wasu fitattun ƴar ƙabilarsa ta Yoruba wadanda suka tabbatar da labarin kamen nasa na cewa suna ƙoƙarin shawo kan hukumomin kasar ta Benin don ka da su amince su taso keyarsa zuwa nan Najeriya.

Misali an ambato shugaban gamayyar kungiyoyin neman ƴancin cin gashin kan al’ummar Yarbawa ta Ilana Omo Oodua Farfesa Banji Akintoye, na cewa shi da sauran masu kishin ƙabilar Yarbawa suna aikin tare domin bai wa Sunday Igboho duk wani taimakon da yake bukata.

Sannan za su tabbatar da babu wanda ya yi masa wani da doka ta hana da kuma hana taso ƙeyarsa zuwa Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here