An kama mutum uku a Masar kan zargin ‘rawa da waƙa a cikin masallaci’

Masallaci a Nijar

Hukumomi a kasar Masar sun kama wasu mutum uku bayan da aka ga ɗaya daga cikinsu a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan zumunta yana rawa da waka a cikin wani masallaci, a cewar rahoton kamfanin labarai na AFP.

An ga wanda ake zargin cikin bidiyon yana rera wata waka da ‘yan kasar ke kira da “mahraganat”. Wakar na cikin jerin wakoki da hukumomin kasar suka hana jin su da kuma saka su a filayen taron jama’a.

Masu suka sun yi Allah-wadai da yadda ake take hakkin dan Adam a karkashin mulkin Shugaba Abdel Fattah al-Sisi, wanda ya hada da kama ‘yan gwagwarmaya da dama a tsawon mulkinsa.

A baya, Masar din ta musanta cewa akwai fursunonin siyasa a cikin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here