Home Sashen Hausa An kama matashi da zargin garkuwa da kuma kashe 'yar shekara 8...

An kama matashi da zargin garkuwa da kuma kashe ‘yar shekara 8 a Kano

An kama matashi da zargin garkuwa da kuma kashe ‘yar shekara 8 a Kano

Daga: Abdulhakim Muktar

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekara 24 da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wata yarinya mai shekara takwas, a cewar rahoton kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN .

An kama Habibu Sale ne ranar 7 ga watan Nuwamba bisa zargin kashe Asiya Tasi’u a ƙauyen Chikawa na Ƙaramar Hukumar Gabasawa duk da cewa ya karɓi kuɗin fansa naira N500,000 daga wurin iyayenta.

DSP Abdullahi Kiyawa, kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne tun a watan Yunin 2020.
Ya ce bincike ya nuna cewa Habibu Sale ya binne gawar Asiya a wani ƙabari da ke wajen garin Chikawa bayan karɓar kuɗin fansar.

An kama matashin ne bayan ‘yan sanda sun yi ta bin sawunsa zuwa jihohin Jigawa da Abia da Kaduna da Katsina da Birnin Tarayya Abuja, a cewar Abdullahi Kiyawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Full Police Statement; on 1/2020

FULL POLICE STATEMENT ; ON 1/2020 ARREST OF THREE MEMBERS OF NOTORIOUS SYNDICATE OF BANDITS/KIDNAPPERS AND RECOVERY OF RANSOM MONEY, THE SUM THREE MILLION AND...

Hukumar Tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci shugaban masu safarar kayan abinci zuwa kudu

Yanzu yanzu: Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci Shugaban masu safarar kayan Abinci bisa dalilin rufe hanya da hana kai kayan Abinci...

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...
%d bloggers like this: