Advert
Home Sashen Hausa An kaddamar da Shirin Allurar rigakafin Dabbobi a Katsina...

An kaddamar da Shirin Allurar rigakafin Dabbobi a Katsina…

A yau Alhamis 11/11/2021, Mai girma Gwamnan jihar Katsina ya kaddamar da allurar rigakafin dabbobi (Kwantangiri) da ake gudanarwa duk shekara a garin Gana Jigawa, cikin karamar hukumar Mashi, shiyar Daura wanda Mai girma Mataimakin Gwamnan jihar Katsina QS Alh Mannir Yakubu ya wakilce shi.
A lokacin da mai girma Gwamna yake jawabi ta bakin mataimakin shi, yace gwamnati ba zatai kasa a gwiwa ba wajen bunkasa kula da kiyon dabbobi tare da inganta lafiyarsu ba duk da matsin tattalin arziki da ake samu, amma insha Allah gwamnati zata cigaba da inganta kiyon dabbobi a jihar, wannan yasa gwamnati take korarin gaske domin cigaba da gudanar da wannan shirin na allurar dabbobi a duk shekara kamar yadda gashi Allah ya kawo mu wannan shekara da zaa gudanar da wannan rigakafi, ya cigaba da cewa kuma akwai shiri da zaa gudanar nan bada jimawa ba na noman ciyawa da samar da wuraren kiyo da samar da asibitin dabbobi da hanyoyi duk duk domin inganta rayuwar makiyaya da dabbobin su.
Haka kuma yace zai dan waiwayo baya domin zayyana wasu nasarori da gwamnatin jihar Katsina ta samu a wannan hukuma, nasarorin sun hada da gina asibitocin kula da lafiyar dabbobi tare da gyara wadanda ke akwai, samar da ingantattun kayan aiki na zamani da samar da magunguna kyauta da dai sauransu.

Tun farko, Dr, Lawal Usman Bagiwa mai ba mai girma Gwamna shawara akan kula da kiyon dabbobi da gandun Daji , yayi godiya ga Allah S.WA da ya nuna mana wannan rana da muka sake haduwa daku a karo na biyu domin gudanar da wannan rigakafin allurar dabobi da zamu fara a yau insha Allah, kana yace ya zama dole muyi godiya ta musamman ga mai girma Gwamnan jihar Katsina RT Hon Aminu Bello Masari abisa goyon baya da yake ba wannan hukuma domin ta gudanar da ayyukan da suke taba rayuwar al’umma kai tsaye, yace yau shekara biyu kenan da mai girma Gwamna ya kirkiri wannan hukuma domin inganta kiyon daddobi a jihar Katsina kuma samuwar hukumar ya samar da cigaba sosai a fannin kiwon dabbobi a jihar Katsina.
Dr Lawal Bagiwa yace a bara sunyi ma dabbobi guda dubu dari bakwai allurar rigafi, kuma wannan shekarar ma insha Allah mai girma Gwmna ya bamu umurnin muyi ma kwatankwacin dubu dari takwas inda kuma zaa kara da rigakafin fakat na kaji insha Allah, haka kuma zaa dauki kwana talatin ,kwana ashirin na manyan dabbobi, kwana goma na kananan dabbobi, haka zalika wannan rigakafi ana yin hada na haukan kare, domin kare lafiyar al’ummar jihar Katsina.
Bagiwa yace kuma akwai shirin noma ciyawa da zasu fara nan bada jimawa ba a kananan hukumomin guda goma da ibti’la’in barayin shanu ya shafa wanda gwamnatin tarrayya ta dauki nauyi.

Taron bikin kaddamar da allarar ya samu halartar manya manya baki da suka hada da Mr .Cort da Mr Martin daga kasar Hongiri, Alh Ya’u Umar Gwajogwajo, shugaban ruko na karamar hukumar Mashi, mai girma Iyan Mashi, hakimin gundumar mashi, Hajiya Jamila Salman Shugabar mata ta jamiyyar APC da sauran manya manyan baki.

Daga Ofis din
Darakta-Janar, Soshiyal Midiya na Gwamnatin Jihar Katsina.
11th Nuwamba, 2021

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...