An Jinjina Wa Likitoci Kan Tsayawa Bisa Ka’idar Aikinsu.

Auwal Isa Musa

Shararren malamin Addinin Musulunci a Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ne ya yi wannan jinjinar a lokacin da yake Tafsirin alkur’ani mai tsarki na watan Ramadhan mai girma a ranar Alhamis din nan da ta gabata.

A lokacin da Malamin ke fassarar Aya ta 36 da ke cikin Suratul Isra’i mai hani a kan bibiyar abin da mutum bai da masaniya a kansa “Wala Takfu ma laisa laka bihi Ilm… (Kar ka bibiyi abin da ba ka da sani a kansa)”, a nan ne Malamin ya bayyana cewa hakika ya cancanta a jinjinawa Likitoci sun ta wannan fannin, domin su ne suka fi kamantawa wajen tsare wannan Ayar da aikata ta fiye da sauran ayyukan da al’umma ke gabatarwa a wasu fannonin.

” A wannan fagen, Likitoci sun cancanta a jinjina ma su.”

“Likita in an zo bakin Iliminsa, zai ce a nan ya sani, bakin ganewarsa kenan; a je wurin wani.”  In ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Shi Likita bai wuce iyakar abin da ya sani, in ko ka ga ya wuce iya abin da ya sani; to karambani ya yi ba haka Iliminsa ya koyar ba. Da an zo inda bai sani ba, zai ce a tambayi wane ko a kara gaba.” Ya ware su.

Ya kara da cewa “Wannan ka’idar (Likitoci) suna tsare ta da kyau sosai, kuma ta yi daidai da (kiyaye) wannan (Ayar).” In ji Malamin

Har wayau, Malamin ya kuma tsoratar dangane da shiga sharo ba Shanun da wasu Ustazai har ma da wasu Malamai ke yi wajen yin katsalandan a cikin abin da ba su da ilimi a kansa, alhali Allah ya hana mutum ya yi magana ko ya yanke hukunci da zargi a kan abin da ba ya da Ilimi a kansa tayadda mutum zai yanke hukunci da zargi ko tsammani cewa a tunaninsa abu kaza haka yake, inda Shehin Malamin ya bayyana cewa wannan babban sabon Allah ne kuma karancin Imani ne, inda ya ce “daga cikin cikar Imanin Mutum, ya tsaya daidai bakin Iliminsa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here