An harbe Nwokorie Anthony, jami’in Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC a Jihar Imo.

An kashe jami’in ne a yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin rijistar zaɓe (CVR) a Ƙaramar Hukumar Ihitte Uboma da ke jihar.

A cewar Kwamishinan Zabe na jihar, Resident, Farfesa Emeka Ezeonu, an kashe Nwokorie ne a Nkwo Ihitte (mazaɓar 004) da ke mazaɓar Amakohia (RA 02) na Ƙaramar Hukumar Ihitte Uboma, sannan ba a san inda wasu ma’aikatan biyu da ke aikin rajistar su ke ba. .

A bisa wannan mumunan lamarin, hukumar zaɓen ta dakatar da gudanar da aikin rijistar katin zaɓen a karamar hukumar.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kaɗa kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Kafin faruwar wannan lamari, hukumar ta dakatar da CVR a Ƙananan Hukumomin Osu da Njaba na jihar saboda rashin tsaro, yayin da ake gudanar da aikin a ofishin INEC na Ƙaramar Hukumar Oru Gabas, Oru ta Yamma, Orlu da Ohaji-Egbema.”

“Hukumar na mika ta’aziyyarta ga iyalan Nwokorie Anthony tare da addu’ar Allah ya basu ikon jure rashin. An kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro domin bankado al’amuran da suka haifar da wannan mummunan lamari tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya,” inji Okoye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here