An haramta sayar da gawayi a Jihar Nasarawa

..

Gwamnatin Jihar Nasarawa a Najeriya ta haramta amfani da sayar da gawayi da kuma amfani da shi a wani yunƙuri na kare muhallin jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito babban sakataren ma’aikatar kula da muhalli na jihar Aliyu Agwai inda ya ce hanyoyin da ake bi wajen samar da gawayi na da illa matuƙa ga muhalli ta hanayar jawo ɗumamar yanayi.

Babban sakataren ya bayyana haka ne a yayin wani jawabi ga manema labarai a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa sare itatuwa zai cutar da wasu dabbobi sakamakon za su rasa wuraren zama wanda hakan zai iya illa ga muhalli.

Ya kuma yi gargaɗi ga masu sayar da gawayin da kuma amfani da shi da su bari ko kuma a kama su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here