An hana hawan Sallah a Daura

Hawan Sallah

Masarautar Daura da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya ta sanar da soke hawan Sallah da ake yi a lokutan salla, saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a wasu sassan jihar.

Galadiman Daura Ahaji Ahmadu Diddiri Ahmadu ne ya tabbatarwa da BBC hakan.

Ya kara da cewa za a yi wata addu’a ta musamman domin neman zaman lafiya mai dorewa a kasa baki daya da zarar an idar da sallar Idi.

“Manufar shi ne kiyaye rayukan jama’a da kuma gabatar da addu’a ta musamman domin ci gaban kasarmu,” in ji Galadima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here