An halattawa ɗalibai sanya hijabi a jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta sanar da amincewa ɗlibai mata a jihar sanya hijabi a makarantu.
Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar kula da harkokin ilimi a ma’aikatar ilimi ta jihar C. K. Olaniyan ta fitar, tana cewa ba a ware makarantu masu zaman kansu a sabon tsarin ba.
Ta kuma yi gargadin cewa matakin na da alaka da wani hukuncin kotu, don haka saɓa dokar na iya zama raina kotu.
Batun sanya hijabi a makarantu ya sha janyo ce-ce-ku-ce a wasu makarantu da ke Najeriya a shekarun baya-bayan nan.