An Gudanar Da Bukin Ba Da Tutoci Na Jam’iyyar APC A Katsina.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis din nan 31 ga Maris, 2022, filin wasan kwallon kafa na karamar hukumar Kankiyar jihar Katsina, ya shaidi bakuncin dubban magoya baya bayan jam’iyyar APC daga kanan hukumomin jihar ta Katsina guda 34.

Taron wanda ya kasance na bayar da tuta ne ga ‘yan takarkarin Ciyamomin jam’iyyar ta APC a daukacin kananan hukumomin, ya samu halartar dubban al’umma Maza da Mata Yara da Manya.

Bukin ba da tutocin dai an soma gabatar da shi ne da misalin karfe 11:00 na safe, inda ya dauki tsawon lokaci kafin a karkare shi, wanda har ya kai karfe 3:00 na yammaci.

Taron, ya tara ‘yan takarkarin kujerar gwamnan jihar da magoya bayansu wanda kowa ya baje kolin nuna kansa a matsayin mai neman kujerar gwamnan jihar a shekarar 2023.

A yayin gudanar da taron daukacin ‘yan takarkari na jam’iyyar ta APC daga kananan hukumomin jihar 34, jiga-jigan jam’iyya tare da masu ruwa da tsaki duk sun halarta.

Haka kuma taron ya samu halartar Shugaban Jam’iyar APC na jihar, mataimaki da Sakatarenshi da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamna Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya bayar da Tutocin ga ‘yan tarkarkarin jam’iyyar, bayar da tutar da bai samu karasuwa gare shi ba sakamakon cinkoson jama’ar da suka dabaibaye wajen, lamarin da ya sa dole gwamnan ya fice daga filin taron.

Saura masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar wadanda suka hada ; Sanata Abubakar Sadiq ‘Yar’adu’a daga karamar hukumar Katsina, Abdullahi Umar Tsauri Tata, Shugaban hukumar tallafawa kanana da matsakaitan sana’o’i Dakta Umar Radda, Mataimakin gwamnan jihar Mannir Yakubu, Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa, Shugaban Bankin ba da Lamuni na Nijeriya Ahmad Dangiwa, Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Faruq Lawal Jo6e, duk sun halarta.

Sauran sun hada da ‘yan Majalisun jiha da na Tarayya, ‘yan jarida da jami’an tsaro, Makada da Mawaka, ‘yan wasan kwaikwayo, da kuma wadanda aka shirya taron don su wato masu neman kujerun Ciyamomin kananan hukumomin jihar 34 da Kansilolinsu da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here