Dahiru Mangal Ya Gina Makarantar Islamiyya Ga Mabiya Kadiriyya A Katsina.

Sanannen Dan Kasuwa Kuma Mai bada tallafin jin Kai a Katsina Alhaji Dahiru Bara’u Mangal,ya gina Makarantar Islamiyya ta Mabiya Kadiriyya A Katsina.

Makarantar dai tana a Unguwar Kofar Yandaka ne tsallaken gidan Marigayi Shakka a nan cikin birnin Katsina.

Kamar yadda Jagoran Yan Kadiriyya na Katsina Malam Ahmed Rufa’i Bayan Day ya shaidawa kafar The Fact 24 wani mai taimakon jin Kai a yankin ne ya samar da filin gina Makarantar a sa’ilinda shi kuma Alhaji Dahiru Mangal ya gina Makarantar.

Bugu da kari,Gwamna Aminu Masari a kashin kanshi ya bayar da gudummuwar kudi da aka sayi wani gida Wanda akayi amfani da shi wurin aikin.

Wannan yunkuri dai na a wani bangare na gudummuwar Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ga kawo cigaban Addinin islama a Jihar Katsina da Najeriya baki daya.

Jagoran Kungiyar ta Kadiriyya Malam Ahmed Rufa’i yayi addu’a akan Allah SWT ya saka da alkairi ya Kuma yi kyakkyawar makoma ga Alhaji Dahiru Mangal da Gwamna Aminu Masari gami da Wanda ya bayar da filin tare da duk wadanda suka bayar da gudummuwa don Gina Makarantar.

Yace suna sane da cewa Makarantar itace ta sama da 200 da Alhaji Dahiru Mangal a gina baya ga masallatai da Kuma sauran ayyukan taimakawa al’umma.

Daga nan sai yayi kira ga sauran masu hannu da shuni akan su Kara kaimi wurin bada gudummuwa ga cigaban addinin Islama domin samun rabauta a nan gidan duniya da ma gobe kiyama.

Wasu daga cikin Yan Kadiriyya da suka maganta sunyi Kira ga al’umma akan su kawo yaransu Makarantar domin samun ilimin addinin Islama.

Sun yabawa jagoran Darikar Kadiriyya na Afrika akan dorasu turba ta gari da soyayyar Annabi SAW.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here