AN GARGADI DAF DAF AKAN TALLAR DAN TAKARA…Kwamishinan kananan hukumomin katsina

Muazu hassan
@ katsina city news
Kwamishinan kananan hukumomin jahar katsina Alhaji yau Umar gwajo gwajo yayi gargadi Daf Daf masu rike da shugabancin kananan hukumomin jahar katsina akan tallar wani Dan takara a jahar .
Kwamishinan yayi wannan gargadin ne, a wani taron gaggawa da ya Kira da Daf Daf din Wanda kuma yace sakon daya ne.wanda an lura wani dan takara an zake wajen tallar shi ana amfani da kayan gwamnati da hukumomin gwamnati da masu rike da mukaman gwamnati.
Don haka su a matsayin su na ma aikatan gwamnati abin da aka sani daga wajen a yanzu da halin da ake ciki aiki da kuma umurnin aiki da aka basu.
Kwamishinan yace don haka zasu Sanya ido kuma a kiyaye.
Wannan umurnin bai rasa nasaba da yadda Babban sakatare a ma aikatan kananan hukumomin katsina ke jagorantar wata kungiya,wadda ke bi gidaje da ofisoshi tana fadin alhairan wani mai sha awar zama gwamnan katsina.
Kuma ana yawan Sanya hotuna bidiyon wannan ziyara da kuma tallar.
Hukuncin babban kotun tarayya ta kasa ta ba ma aikacin gwamnati yancin yin siyasa.amma a hukuncin Wanda jaridunmu suka gani ta bada wasu hannunka mai sanda cikin shi harda maganar tallar dan takara kafin lokacin da hukumar yakin neman zabe ta bada, a fara kamfen.
Masu neman gwamna a katsina suna da yawa.amma duk sun tsaya ne a tattaunawa da tuntuba. Wanda wannan ba laifi bane.
Mutum daya ne aka zake akan shi.an fara buga fastoci ana likawa duk shatale talen katsina.an buda ofis ofis har da wani a tsakiyar birnin katsina bisa titin yahaya madaki ana yawo da motoci masu hotuna.ana taro har a cikin ofis jam iyya ta jaha.inda wasu matasa sukayi.gidan sa ya zama kama sati uku masu zuwa za ayi zabe.ana tsorata ma aikatan gwamnati cewa in kana son tsira da aikin ka to ka bishi.
Wadannan matakan da aka fara dauka zasu taima wajen Sanya natsuwa a harkokin siyasar ta jahar katsina.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here