Daga: Surajo yandaki
Edita, Mobile Media Crew

Bayan samun labarin, gano wajen hako zinari a yankin Zandam dake cikin karamar hukumar Jibia cikin Jihar Katsina.

Wata tawaga ta musamman daga Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Jagorancin Kwamishinan ma’aikatar kula da ayyukan kananan hukumomi da masarautu na Jihar Rt. Hon. Ya’u Umar Gwarjo, gwajo ta ziyarci wajen ranar Asabar 27/11/2021, Domin ganema idanunta.

Inda tawagar ta samu jama’a da dama wanda mafi akasarinsu matasa ne, sunata gudanar da wannan harka ta hakar Zinari, Yayin ziyarar Kwamishinan ya bayyana ma masu hakar Zinarin cewa”, Gwamnatin Jihar Katsina ce ta turo su domin suzo su duba su gani yadda ake tafiyar da wannan harka da hakar Zinari, a wannan wuri.

Badon komi ba, sai don Gwamnati ta dauki matakan kula da lafiya da kuma tsaro gareku, da kuma tanadar maku hanyar baku horo na musamman akan wannan harka ta hakar Zinari a zamanance. Mai girma Kwamishinan ya cigaba da bayyana masu cewa” su kwantar da hankalin su, kuma suyi biyayya da irin tsare, tsaren da Gwamnati zata bullo dasu.

Domin Gwamnati batada gurin tada kowa saima bullo da hanyoyin da zasu inganta wurin, ya kuma basu tabbacin Gwamnati a shirye ta ke ta taimaka ma rayuwar Al’umma musamman Matasa ta kowane bangare muddin abinda sukazo da shi bai sabama Dokokin kasa ba.

A cikin tawagar Kwamishinan akwai Darakta mai Kula da harkar ma’adanan kasa na ma’aikatar kula da Albarkatun kasa ta Jihar Katsina, Kwamishinan da tawagarsa ya samu tarba daga Mai rikon karamar hukumar Jibia, da Dagacin yankin Zandam na karamar hukumar Jibia. Dadai sauransu.

Al’ummar dake hakar Zinarin sunyi godiya tare da yabo ga Gwamnatin Jihar Katsina akan kulawar gaggawa da su ka samu da kuma albishir da aka basu, sun kuma yi alkawalin yin biyayya da duk tsari da Gwamnati tazo da shi.

27 November, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here