Najeriya: An Dage Zaman Sauraren Shari’ar Sheikh Zakzaky Da Maidakinsa Zuwa Gobe Talata

Bin Muhammad

Kotun da ke sauraren shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harka Islamiyya a Najeriya da mai dakinsa, ta dage zaman sauraren shari’ar da aka gudanar a yau Litinin, zuwa gobe Talata.

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, Kotun da ke sauraren shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harka Islamiyya a Najeriya da mai dakinsa Malama Zeenat Ibrahim, ta dage zaman sauraren shari’ar zuwa gobe.
A zaman na yau dai kotun ta saurari wasu daga cikin shedun gwamnati ne, da suka hada da jami’an tsaro, inda kuma a zaman da za a gudanar gobe kotun za ta bayyana abu na gaba, kamar yadda dukkanin lauyoyin da suke cikin tawagar lauyoyi masu kare Sheikh Zakzaky sun halarci karkashin jagoran lauya Femi Falana SAN.
A wani labarin kuma kotun ta amince da sakamakon gwajin corona da aka yi malama Zeenat Ibrahim, wanda ke tabbatar da cewa, tana dauke da cutar.
A rahoton da tashar Channelstv ta bayar, ta bayyana cewa kotu ta bayar da umarni ga jami’an da ke kula da gidan kason Kaduna, da su dauki Malama Zeenat Ibrahim zuwa wurin da ake killace jama’a da suke dauke da cutar domin a kula da ita.
Tun a ranar Alhamis da ta gabata, a wata zantawa da ya yi da tashar talabijin ta Channels tv, shugaban dandalin yada labarai na Harka Islamiyya Malam Ibrahim Musa ya yi bayani kan sakamakon gwajin da aka yi wa Malama Zeenat Ibrahim, wanda ke tabbatar da cewa tan adauke da cutar.
Sai dai jami’an gidan kason na Kaduna tun daga lokacin fitar da sakamakon suka karyata hakan, inda suka bayyana rashin amincewarsu da sahihancin sakamakon gwajin, amma yanzu bayan umarnin da kotu ta bayar, sun amince da sakamakon gwajin.
Kafin wanann lokacin Muhammad Ibrahim Zakzaky dan Sheikh Ibrahim Zakzaky ne ya fara fitar da sanarwa, kan cewa mahaifiyarsa da ke tsare tana fama da cutar corona a cikin gidan kaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here