Daga Auwal Isah. @Katsina City News
Gwamnatin jihar katsina, ta dage dokar nan ta tsagaita zirga-zirga da ababen hawa masu kafa biyu a fadin jihar.
Sanarwar dage dokar wadda jami’in hulda da jama’a na jami’an ‘yan sandan jihar, Gambo Isah ya fitar a yau Juma’a, ta bayyana cewa an dage dokar ne a dalilin zuwan Azumin watan Ramada, watan da ake zirga-zirga da kara yawaita Sallolin Tahajjudi da sauran Ibadodin neman kusanci ga Allah(T)
“Ina mai bada sanarwar dage doka wadda aka sa ta hawa babura a cikin birnin Katsina wadda take farawa daga karfe 10:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe.” In ji shi
“Har ila yau, da dokar da aka sa ta kananan hukumomi masu fuskantar barazana wadda take farawa daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na Asuba (ita ma an janye ta)”
Gambo Isah, ya kara da cewa, “Saboda wata mai albarka da za mu shiga na Ramadana, an dage wannan doka zuwa bayan Azumi.”
“An dage dokar ne domin jama’a su sami dama na zuwa su yi sallar Tarawih, su je wurin Tafsirai da ake gabatarwa na karatun Alkur’ani da Fassara, da kuma Sallolin Tahajjudi.”
Indai ba a manta ba, a ranar 16 ga watan Janairun 2022 ne, gwamnatin jihar ta katsina ta sanya wasu dokoki daga ciki hada hana zirga-zirga da ababen hawa masu kafa biyu a fadin jihar dokar ta rika farawa daga 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a yunkurinta na yaki da barayi masu garkuwa da mutane wadanda suke fakewa da babura wajen tafka ta’asa, dokar da a baya aka rika sassauta ta har ta dawo daga 10:00 dare zuwa 6:00 na safe.