Advert
Home Sashen Hausa An ci tarar gidajen talabijin na Channels, AIT, Arise kan zanga-zangar EndSARS

An ci tarar gidajen talabijin na Channels, AIT, Arise kan zanga-zangar EndSARS

An ci tarar gidajen talabijin na Channels, AIT, Arise kan zanga-zangar EndSARS

NBC

Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta NBC a Najeriya ta ci tarar gidajen talabijin na Channels da AIT da Arise game yadda suka yi rahotanni kan zanga-zangar EndSars.

Muƙaddashin daraktan hukumar Farfesa Armstrong Idachaba, shi ne ya bayar da sanarwar tarar a yau Litinin a Abuja, inda ya ce za su biya tarar naira miliyan uku kowannensu.

An yaɗa hotuna da bidiyo na boge a tsakanin mako biyu da aka shafe ana zanga-zangar nuna ɓacin rai game da ayyukan rundunar ‘yan sanda a Najeriya, wadda aka yi wa laƙabi da EndSars – wato a rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami.

BBC ta bincika tare da bankaɗo gaskiya da ƙaryar wasu daga cikinsu.

An ci tarar gidajen talabijin ɗin uku ne saboda “yaɗa hotunan da ba a tantance ba na harbe-harben da ake zargin an yi”.

Tun a baya, NBC ta gargaɗi kafofin yaɗa labarai da su yi taka-tsantsan wurin yaɗa hotunan da suka samu daga shafukan sada zumunta, tana mai cewa rashin tantance sahihancinsu ka iya jawo hatsaniya a ƙasa baki ɗaya.

Social embed from twitter

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

DRAFT APC CONVENTION TIMETABLE – Jan 16, 2022

1. January 17th - PMB Letter to CECPC on February National Convention and associated matters 2. January 18th -CECPC Meeting announcing National Convention date of...

Da ƊUMI-ƊUMI- Kotu ta umarci Rundunar Sojin Ƙasa da ta baiwa Nnamdi Kanu Naira biliyan 1

Wata Babbar Kotu da ke zaman ta a Umuahia ta baiwa Gwamnatin Taraiya da Rundunar Sojin Ƙasa da su baiwa Jagoran masu Rajin Samar...

THE RECONSTRUCTION OF THE APAPA – OWORONSHOKI – OJOTA EXPRESSWAY IS PROGRESSING EXPRESSLY!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/258361216380403/

Teenager kills man over football league supremacy

Teenager kills man over football league supremacy By Danjuma Michael, Katsina 19 January 2022   |   2:53 am A teenager, Idris Yusuf, 18, has allegedly killed a...