An Cafke Ɓarawon Da Ya Saci Sadaki Naira Dubu 100, Ana Cikin Ɗaurin Aure A Masallaci

A jiya Juma’a bayan idar da Sallah a masallacin Juma’a na Al-Noor dake titin IBB Wuse 2 Abuja an kama wani Barawo da ya sace kudin Sadaki a dai-dai lokacin da ake daura Auren wata budurwa da Saurayinta.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, sadakin ya kai Naira Dubu Dari. Sai dai an karbi sadakin daga hannun barawon inda ya sha duka a hannun masu tsaron masallacin.

Sannan ya yi nadama bisa ga abinda ya aikata.Wannan shi ne karo na biyu da aka taba sace kudin sadaki a wannan masallacin.

An dai sace kudin kafin a biya sadakin wanda ya yi sanadiyar daura auren bashi sai daga baya angon ya sake samun kudin ya biya sadaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here