Advert
Home Sashen Hausa An Bukaci Jam'iyar APC ta kasa ta ladabtar da Yari da Kabiru...

An Bukaci Jam’iyar APC ta kasa ta ladabtar da Yari da Kabiru Marafa — Abdullahi Shinkafi

Hoto: Sanata Marafa da Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Daya daga cikin fitattun ‘yansiyasar jihar Zamfara kuma tsohon dankaran gwamna a jam’iyar APGA, kuma mamba a jam’iyar APC, Alh Abdullahi wamban Shinkafi, ya yi kira ga uwar Jam’iyar su ta APC data hukunta Abdul’aziz Yari da Kabiru Marafa saboda karya dokar da ke cikin kundin tsarin mulkin jam’iyar.

Shinkafi ya yi wannan kiran ne ga manema labarai a Gusau , babban birnin jihar, ya ce hakan ya biyo bayan taron da su Abdul’aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa da wasu ‘yayan jam’iyar suka yi a Kaduna , bayan ficewar gwamna Bello Mohammed Matawalle da magoya bayansa daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyar APC a hukumance a ranar Talata da ya gabata.

Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya bukaci a kaka bawa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar takunkumi mai tsauri saboda sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, ya ce dole ne a dauki tsauraran matakai a kan Yari da kabiru Marafa .

Ya bayyana taron da Yari da Kabiru da magoya bayansu suka yi a Kaduna inda suka yi tir da umarnin shugabannin jam’iyyar na kasa kan rusa shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai a jihar da cewa cin fuska ne ga Shugaba Muhammadu Buhari da dukkanin shugabannin jam’iyyar na kasa.

Ya kara da cewa aiyukan da Abdul’Aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa suka yi karara sun karya doka ta 21 (a), (iii) da (iv) na Kundin Tsarin Mulki na Jam’iyyar ( APC ) All Progressives Congress na 2014 kamar yadda aka gyara.

Ya ce “Mataki na 21 na kundin tsarin mulkin APC ya tanadi ikon ladabtar da mambobin jam’iyyar , ya ce “Za a yi amfani da Ikon ne a madadin Jam’iyyar ta kwamitin zartarwa na Jam’iyyar a dukkan matakai.

“Musamman, Mataki na 21 (a) ya tsara cewa” Laifi ne kan ‘ya’yan Jam’iyyar su aikata waɗannan lefuka: i. Keta duk wani tanadi na wannan Kundin Tsarin Mulki. ii. Ayyukan Anti-Party ko duk wani hali, wanda da alama zai kunyata ko ya haifar da illa a cikin jam’iyyar ko kuma kawowa jam’iyyar cikin ƙiyayya da raini da izgili ko rashin mutunci. iii. Rashin biyayya ko sakaci wajen aiwatar da halaye masu kyau na Jam’iyyar .

Shinkafi ya ce Yari da Marafa da magoya bayansu su lura cewa babu wata kungiya da ta fi karfin doka saboda haka umarnin da shugaban jam’iyar riko na kasa, MaiMala Buni ya bayar na rusa shugabannin jam’iyyar na jihar tun daga kananan hukumomi har na jihar da kuma bayyanawa al’umma cewa Gwamna Matawalle a matsayin shugaban APC a Zamfara .

“Tun daga ranar 29 ga watan June 2021, an bai wa gwamna Matawalle mukamin shugaban jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara, saboda haka, duk wani matakin da kowane dan jam’iyyar zai dauka ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

“Na yi mamakin cewa bayan Yari wanda ya gaya wa duniya cewa zai goyi bayan Matawalle don gina jam’iyyar, yanzu zai iya komawa Kaduna ya sake yin wani taron yana kalubalantar Shugaban jam’iyar na riko Maimala Buni , ya ce yunkurin Yari da Marafa na raba kan APC , saboda haka ya bukaci shugabannin jam’iyyar na kasa da su dauki tsauraran matakai don ceto jam’iyyar daga masifar 2019.

Wambai ya bukaci jami’an tsaro su sanyawa Yari da Marafa da magoya bayansu ido kar su sami damar wargaza babbar jam’iyyarmu, ya ce “Yari da magoya bayan sa su sani cewa a yanzu mu mambobin kungiyar masu kishin kasa ne a APC saboda haka, ba za mu rungume hannu mu kalli wasu fusatattun abubuwa da za su bata jam’iyyar mu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

COURT IN KATSINA CONVICTED INTERNET FRAUDSTERS.

@ katsina city news The Kano Zonal Command of the Economic and Financial Crimes Commission today August 5th, 2021 secured the conviction of eight internet...

Rashin tarbiya; Dalibi ya daba wa malaminsa wuka har lahira, saboda kawai malamin ya yi masa bulala

A makarantar sakandaren koyar da fasaha dake Bukuru ‘Government Technical College Bukuru (BUTECHS)’ dake jihar Filato ne wani dalibi ya kashe malaminsa saboda malamin...

Ƴan Bindiga Sun Sace Mahaifan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim,Gusau "Yan bindigar sun mamaye garin Magarya garin kakakin majalisar jihar Zamfara Nasiru Mu'azu Magarya da yammacin ranar Laraba inda suka yi awon...

Kowa Na Da Rawar Da Zai Taka Wajen Samun Dawammamen Zaman Lafiya A Najeriya, Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ba jami'an tsaro ba ne kadai ke da hakkin samar da tsaro a kasar...
%d bloggers like this: