Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas a majalisar dokokin kasar, Mohammed Musa, ya ce ya kamata jami’an tsaro su gayyaci fitaccen malamin addinin musulunci nan, Sheikh Ahmad Gumi, domin yi masa tambayoyi kan alakarsa da ‘yan bindiga.

Sanatan, ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels a yammacin ranar Talata.

Ya kara da cewa Gumi yana ganawa da wadannan ‘yan fashin a cikin dazuzzuka don haka ya kamata ya baiwa gwamnatin Najeriya bayanan da za su taimaka wajen dakile ayyukansu.

“Ba zan ce mun san yan fashin ba. Amma abinda muka ce, suna da kungiyoyi kuma suna da nau’in tsarin jagoranci a cikin kungiyoyin na su, “in ji shi.

“Zan iya tuna cewa daya daga cikin fitattun malaman addinin musuluncin ƙasar nan, Sheikh Gumi, a wani lokaci yana shiga dazuka domin ganawa da wadannan mutane.

“Ina ganin ya kamata a tambayi wani kamar Gumi yadda yake tuntuɓar mutanen nan. Idan har zai iya kai wa ga wadannan mutanen, me ya sa ya kasa taimakawa gwamnati wajen ganin an raba mutanen nan da zama cikin tsaka mai wuya?”

Sanata Musa, ya ce matsalar tsaro ta kara ta’azzara a jihar Neja yayin da ‘yan ta’addan da suka koma Zamfara suka sake dawowa jihar domin gujewa ayyukan soji da ke addabar su jihar ta Zamfara.

“Mun sami kwanciyar hankali a cikin watanni biyu da suka gabata, amma yanzu, sun dawo kuma sun kasance marasa tausayi. Don haka muna kuma son gwamnati ta yi musu rashin tausayi,” ya kara da cewa.

Kuna tuna cewa kwanaki biyu da suka gabata ne Jaridar Sokoto ta ruwaito malamin acikin wata sanarwar da ya fitar yana gargadin gwamnatin tarayya da ka da tayi kuskuren ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda ya mai cewa; da zarar an ayyana ƴan bindigar a matsayin ƴan ta’adda ƙungiyoyi masu da’awar jihadi na ƙasashen waje za su samu gindin zama.

A wani bangare na sanarwar malamain ya ce ayyukan da ƴan bindigar ke aikatawa sannu a hankali sun zama na ta’addanci, “saboda duk inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, ta’addanci ne tsantsar sa.”

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here