AN BUDE SABUWAR MAKARANTAR KUDI TA ILIMIN ZAMANI A GARIN DAURA.

AL-KHAIR INTERNATIONAL ACADEMY DAURA.
TA RENON YARA (NURSERY)DA PRIMARY.

An bude makarantar a cikin gininta na din din din a harabar makarantar Ihya’us Sunnah kusa da Gen. Muhammadu Buhari Primary School, domin samar da ingantaccen ilimi na zamani da harshen turanci tare da ilimin na’ura mai kwakwalwa (Computer) ta hanyar Samar da kwararrun malamai a fanni daban-daban.
Har an fara sayar da takardar neman shiga Makaranta akan kudi N1000 kacal na zangon farkon shekarar karatun(2021).
Dukkan mai bukatar yaransa su sami nagartaccen ilmin zamani (boko) hade dana addini akan tarbiyya mai kyau, ya hamzarta ya garzayo harabar Makarantar: Madrasatu Ihya’is Sunnah Wa-ulumil Islam Baraji Daura,
wadda take kusa da Daura One Primary School Daura, karka bari abar iyalanka abaya, sayen nagari maida kudi gida.
Domin neman karin bayani sai atuntubi shuwagabannin gudanarwa a wadannan lambobin kamar haka:- 09039795176,-08065614266.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here