AN BUDE MAKARNTAR MASU AMFANI DA SOCIAL MEDIA!!!

MAKARATAR HASSAN USMAN KATSINA POLYTECHNIC, TAYI TARON BUDE KARATUN WATA UKU GA DALIBAN FARKO DA MAI GIRMA GWAMNA YA DAUKI NAUYI NA MASU AMFANI DA KAFAR SADA ZUMUNTA TA ZAMANI (SOCIAL MEDIA) WANDA ZAI BAIWA DALIBAN DAMA ZAMA HALATTATUN YAN JARIDA.

Makarantar Hassan Usman Katsina Polytechnic tayi taron bude sashen  masu amfani da kafar sada zumunta na wata uku (Three Months Social Media Certificate) na dalibai 100 a karon farko, wanda mai girma Rt Hon Dr Aminu Bello Masari ya daukin nauyi karkashin ofishin mai bashi Shawara akan harkokin Siyasa Hon Kabir Shaaibu Charanchi

Taron ya samu halarcin Shugaban Makarantar, Malamai da shuwagabannin shiyoyin karatu daban daban na ciki da wajen makarantar, Director Political Affairs wanda ya wakilci Hon Kabir Shaaibu (Special Adviser on Political Matters) dalibai da Allah ya baiwa dama shiga karatun na farko da sauran muhimman mutane daga bangarori daban daban.

Dr Mukhtar El-kasim wanda shine shugaban bangaren horar da aikin Jarida (HOD Mass Communication Department) ya jaddada tare da haska yadda tsarin karantun zai kasance bisa tsari, doka da bin hanyoyin da daliban zasu samu fahimta, ya kara da baiyana cewa wannan karantu zai baiwa wadanda suka samu damar shiga, zama halattatun yan Jarida kuma zasu iya rijista da kungiyar ta yan Jarida watau Nagerian Union Of Journalist (NUJ).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here