A yau Laraba ne a ka binne marigayi Sani Ɗangote, ƙani ga Aliko Ɗangote, a maƙabartar Alhasawa ta dangin Ɗantata da ke unguwar ƙoƙi a cikin birnin Kano.

Manyan baƙi je dai da su ka haɗa da tawogar Shugaban Ƙasa, gwamnoni, Shugaban Majalisar Dattijai, Ministoci, Sarkin Kano da manya-manyan ƴan kasuwa.

Sauran sun haɗa da tsofaffin gwamnoni da tsohon Shugaban Majalisar Dattijai da sauran manyan baƙi.

Babban Limamin Masallacin Ƙofar Kudu ne ya ja sallar jana’izar a daidai ƙarfe 10:05 na safe a farfajiyar fadar Sarkin Kano.

Marigayin ya rasu ne a wani asibiti a birnin Miami na ƙasar Amurka.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa, matarsa, ƴaƴa da kuma ƴan uwa da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here